Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a sake bitar shari’ar Sojojin Najeriya da aka yanke wa hukunci

Rundunar tsaron Najeriya ta ce za a sake bitar wasu daga cikin shari’o’in da aka yi wa sojojin kasar da ake zargi da gudu daga fagen daga da kuma wadanda suka aikata laifufuka daban daban.

Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram REUTERS/Joe Penney
Talla

A cewar mataikamin shugaban sashen yada labarai na rundunar sojan kasar Kanal Sani Usman Kukasheka za a sake nazarin shari’ ar da ake wa wasu sojin kasar bisa korafe korafen da rudunar Sojin ta samu.

Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa za a bi shari’o’in ne dalla dalla domin yanke hukuncin da ya dace.

Sai dai ya ce wannan ba mataki ba ne da zai sa a dawo da wasu Sojojin da aka kora ba illa za a sake yin nazarin zargin da ake masu da kuma hukuncin da aka yanke masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.