Isa ga babban shafi
Uganda

Kotun Uganda ta haramta maidawa maza kudin sadaki

Kotun kolin kasar Uganda ta zartar da hukuncin haramta maidawa maza kudin sadaki bayan mutuwar aure.Yau dai ta kasance tamkar sallah a ko’ina, inda kungiyoyi na mata da jama’a ke ta ruguntsumin murna bayan da Kotun kasar wadda daga ita sai Allah ya isa ta zartar da wanna hukuncin.

REUTERS/Edward Echwalu
Talla

Kotun dai ta ce daga yanzu kada a sake Ji ko ganin an biya wani kudi ko kayan sadaki muddin aka samu mutuwar aure.

Kotun ta ce ta soke biyan ne domin ko kadan babu haka a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Matakin dai ya biyo bayan kararraki da kungiyoyin mata suka shigar tun daga karamar kotu har kotun koli, inda suke nuna da cewa mata su biya abinda miji ya kashe akansu na matukar haifar da fitina tsakanin dangi da ‘yan uwan ma’aurata a fadin kasar.

Kungiyoyin mata da ke ta bukukuwan murna a kasar yau alhamis, sun ce mata yanzu a fadin kasar hankalin su zai kwanta, domin muddin suka ga gidan da suke ba wurin zaman aure bane, babu abinda zai sa mace ta zauna.

Tun dai a shekarar 2007 ake ta takaddama a game da wannan batu na sadaki, inda kungiyoyin mata a kasar ke cewa wasu mazajen na kashe makudan kudade a lokutan aure ta yadda matan ba sa iya biya idan rabuwa ta taso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.