FPI ta zabi Nguessam dan takararta a zaben shugabancin Ivory Coast
Jam’iyyar FPI, ta tsohon shugaban Cote D’ivoire Laurent Bagbo ta zabi Pascal Affi Nguessam a matsayin dan takarta a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 25 ga watan oktoban wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Wakilan jam’iyyar sama da dubu 4 ne suka halarci wani gagarumin taro a jiya asabar a garin Trecheville, inda suka zabi Nguessam wanda ke rike da mukamin shugabancin jam’iyyar na kasa.
N’Guessam ya bukaci magoya bayan tsohon shugaba Bagbo wanda ke tsare a hannun kotun duniya, da su jefa masa kuri’unsu a zaben mai zuwa, inda ya ce hakan na a matsayin nuna karamci ga tsohon shugaban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu