Isa ga babban shafi
Kamaru

‘Yan sandan Kamaru sun ceto Yara 72 da ake garkuwa da su

‘Yan Sanda a kasar Kamaru sun ce sun kubutar da wasu yara kimanin 72 da wani malamin addinin Islama ya yi garkuwa da su a samamen da suka kai wata makarantar Islama a arewacin kasar.

Bataliyar Sojin Kamaru da ke fada da mayakan Boko Haram
Bataliyar Sojin Kamaru da ke fada da mayakan Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

‘Yan Sandan sun ce yayin samamen a Ngaoundare, sun gano Yan Najeriya 17 da ke zama cikin kasar ba tare da izini ba, wadanda suka hada da mata 10, namiji guda da yara 6, tare da wasu Yan Kamaru 19 wadanda ba su da takardar shaidar dan kasa.

Jami’an tsaron sun ce sun samu wasu daga cikin yaran daure da Mari a kafafuwan su.

Wata majiya ta shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa malamin na koyar da yaran ne karatun Al Qaur’ani a kamar fursunoni.

Yanzu Jami’an tsaron Kamaru za su tatsi bayanai daga bakin yaran da aka kubutar domin jin abin da ya faru.

Kamaru dai ta inganta tsaro domin farautar Mayakan Boko Haram da ke addabar yankin arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.