Ana yaki da cutar Kansa a Nijar
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da yaki da cutar Kansar Mama da mahaifa ta hanyar gwaji da kuma yekuwa don dakile yaduwar cutar da ta shafi mata.
Wallafawa ranar:
Issimouha Dille, jami’an lafiya a birnin Yammai yace matsalar cutar abin tsoro ne a Nijar yayin da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace a kowacce shekara ana samun sabbin wadanda suka kamu da cutar 8,000.
Bayanai sun nuna cewar kashi 27 na wadanda suka kamu da cutar suna fama da Kansar Mama ne, sai kuma Kansar mahaifa kashi 14, kamar yadda kididdigar asibiti ta bayyana.
Dille ya ce wasu matan kan ziyarci bokaye don samun magani abin da ke sanadiyar mutuwarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu