Isa ga babban shafi
Libya

Libya na son kasashen Larabawa su kaddamar da hari akan IS

Gwamnatin Kasar Libya da kasashen duniya suka amince da ita ta bukaci kasashen Larabawa su kaddamar da hare haren sama a birnin Sirte, mahaifar tsohon shugaban kasa Muammar Ghadafi don kakkabe mayakan ISIS da suka mamaye garin.

Dakarun Gwamnati Libya da ke fada da 'Yan tawaye a lardin Derna
Dakarun Gwamnati Libya da ke fada da 'Yan tawaye a lardin Derna REUTERS/Stringer
Talla

Halattaciyar Gwamnatin ta bukaci gwamnatocin kasashen larabawa su kai ma ta dauki bayan ta yi zama na musamman kan bukatar.

Mayakan IS da ke da’awar jihadi na ci gaba da zama barazana a Libya, wadanda suka samu shiga saboda rabuwar kasar gida biyu.

Yanzu haka bangarori biyu ke jagoranci a Libya wadanda ke ci gaba da hamayya da juna.

Libya dai ta fada rikici tun kawar da gwamnatin Marigayi Kanal Ghaddafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.