Isa ga babban shafi
Libya-Algeriya

Ana ci gaba da neman hanyar kawo karshe rikicin kasar Libya

Ministan harkokin Africa na kasar Algeria, tare da Ministocin harkokin waje na kasashen Niger da Chadi suna wani taro a birnin Algiers, da nufin gabatarwa Libya mafita daga rikicin da kasar ta sami kanta.

Dakarun Gwamnatin kasar Libya
Dakarun Gwamnatin kasar Libya REUTERS/Stringer
Talla

Ministocin suna fatan baiwa bangarorin dake rikici da juna a kasar su duba yuwuwar samar da gwamnatin hadin kan kasa, don shawo kan kalu balen da take ci gaba da fuskanta.
Cikin wata sanrwar hadin gwiwar da suka sanya hannu, ministocin kasashen wajen, Abdelkader Messahel, Aichatou Kane Boulama da Moussa Faki Mahamat sun bayyana cewa sanya hannun kasashen ketare zai taimaka a kawo karshen matsalar ta kasar Libya.
Kasar Libya wadda ta yi iyaka da kasashen uku na cikin rudani ne tun baya dakarun kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN, sun jagoranci kawar da Gwamnatin marigayi Shugaba Moammar Gaddafi.
Libya, dake arewacin nahiyar Afrika, nada majakisun dokoki 2, dake zaman doya da manja, daya dake birnin Tripoli, da wadda kasashen duniya suka amince da ita, dake gabashin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya na fatan ganin wannan tattaunawar ta samar da mafita kan rikicin na Libya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.