Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu na son a sa ido ga yarjejeniyar tsagaita wuta

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi kira ga kasashen da ke shiga tsakanin rikicin kasar su sa ido ga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ‘Yan tawaye, tare da yin watsi da ikirarin ta saba yarjejeniyar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Sudan ta kudu da ‘Yan tawaye dai na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a ranar 29 ga watan Agusta, da nufin kawo karshen rikicin kasar da aka shafe sama da watanni 20 suna yaki.

Amurka ta ce tana shirin kakabawa shugabannin bangarorin biyu takunkumi akan saba yarjejeniyar tsagaita wuta.

Wakilan Kungiyar kasashen gabashin Afrika IGAD wadanda ke taka rawa wajen sasanta rikicin kasar za su ci gaba da sa ido domin tattabatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince a Addis Ababa.

A watan Disemban 2013 ne Sudan ta kudu ta fada cikin rikici tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaban kasa Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Rikicin kasar kuma ya rikide ya koma na kabilanci tsakanin kabilar Dinka ta Kiir da kabilar Nuer ta Machar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.