Boko Haram ta kashe mutane 9 a Kolofata cikin Kamaru
Akalla mutane 9 suka mutu yayin sama da 20 suka jikkata a wasu hare haren kunar bakin wake guda biyu da aka kai a garin Kolofata arewacin Kamaru a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ana kyautata zaton Mayakan Boko Haram ne suka tayar da bama baman.
‘Yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman ne da ke jikinsu a lokacin da ‘Yan banga suka tunkare su bayan sun nufi kasuwa.
Wada Alhaji wani Dan jarida a Kamaru ya shaidawa RFI Hausa cewa ‘Yan banga da aka daura wa alhakin tsaro a Kolafata ne suka gano ‘Yan kunar bakin waken guda biyu daure da bama bamai a jikinsu
A cewarsa sun tayar da bama baman ne a lokacin da aka nemi a kama su.
Garin Kolafata dai na kan iyaka ne da yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da Boko Haram, kuma an dade mayakan na kai hare hare a garin.
Kasar Kamaru na cikin rundunar kawance 5 da suka hada da Najeriya da Chadi da Nijar da Benin da ke tunkarar mayakan Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu