Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Manyan hafsoshin Sojin Burkina Faso na shirin kwace mulki daga Diendere

Yanzu haka ayarin sojoji daga sassa daban daban na kasar Burkina Faso, sun doshi birnin Ouagadougou fadar gwamnatin kasar, kuma sanarwar hadin guiwa da suka fitar a dazun nan, manyan kwamandojin sojin kasar sun ce za a kwancewa wadanda suka yi juyi mulki damara ta ruwan sanyi ne. 

Sojojin Burkina Faso kan hanyar su na zuwa Ouagadougou
Sojojin Burkina Faso kan hanyar su na zuwa Ouagadougou REUTERS/Joe Penney
Talla

Rahotanni sun ce ayarin sojoji daga garuruwan Dedougou da kuma Bobo Dioulasso da ke yammacin kasar, da wani ayarin wanda ya taso daga Kaya da Fadan Gourma a bangaren gabas sai kuma wasu sojojin daga Ouahigouya daga arewaci ne suka nufi birnin na Ouagadougou kuma suna dauke ne da manyan makamai.

Wadannan sojoji ba sa goyon bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, lamarin da ke faruwa a dai dai lokacin da tawagar kungiyar kasashen yankin yammacin Afrika ECOWAS-CEDEAO ta bakin shugaban hukumar ta zartaswa Kadre Desire Ouedrago ke cewa an cimma jituwa da sojojin kan yadda za a dawo da gwamnatin rikon kwarya akan madafan iko a wani daftari mai kunshe da sharudda 13.

Ra’ayoyi dai sun sha bamban dangane da wannan yarjejeniya da aka cimma bayan share tsawon yini uku ana tattaunawa tsakanin sojojin da kuma shugaban kungiyar Ecowas shugaban Senegal Macky Sall, musamman ma dage tsawaita wa’adin gudanar da zabe a maimakon 11 ga watan oktoba zuwa 22 ga watan nowamba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.