Diendere ya bukaci Sojoji su mika wuya
Shugaban Sojin da ya jagoranci juyin mulkin kasar Burkina Faso Janar Gilbert Diendere ya sanar da cewar an kawo karshen harin da sojojin da ke yiwa gwamnatin kasar biyaya suka kai kan dakarun sa a barikin su da ke Ouagadougou.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da jagoran juyin mulki Janar Gilbert Diendere ya yi, ya bukaci magoya bayan sa da su aje makaman su dan kaucewa zub da jinni a ciokin kasar.
Rahotanni sun ce anji karar fashewar manyan makami a barikin sojojin dake gadin fadar shugaban kasar, sakamakon kawanyar da sojojin dake biyaya ga gwamnatin farar hula suka musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu