ICC za ta fara shari'ar Al-Faqi na Mali
A yau laraba ne ake saran kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya dake Haque za ta fara sauraron tuhumar da ake yiwa Ahmad Al-Faqi Al-Mahidi, daya daga cikin shugabannin 'Yan Tawayen Mali da ake zargi da lalata wuraren tarihin a Timbuktu.
Wallafawa ranar:
Za a tuhumi Al- Faqi, shugaban wanda ake kira Abu Tourab da laifuffukan yaki kuma a karon farko kenan da zai bayyana a gaban Kotun tun bayan da sojojin Jamhuriyyar Nijar suka mika shi ga jami’an kotun a ranar Asabar
A watan Yunin bara ne Yan Tawayen Ansaruddine da Al-Faqi ke jagoranta suka lalata wuraren tarihi da suka hada da makabartar Shaihunan malamai na karnin 15 da 16.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu