Isa ga babban shafi
EU-Guinea

EU ta ce akwai Sahihanci a Zaben Guinea

Kungiyar Kasashen Turai ta ce akwai Sahihanci a Zaben Shugabanci kasar Guniea, duk da irin matsalolin da aka samu a lokutan zaben da ake saran Shugaba mai ci, Alpha Conde ya sake komawa Mulki a karo na 2.

Shugaban Guinea Alpha Condé
Shugaban Guinea Alpha Condé AFP/CELLOU BINANI
Talla

Sanarwar da Kungiyar ta Fitar na zuwa ne bayan barkewar rikici da ya biyo bayan zaben kasar da aka gudanar a ranar Lahadi tsakanin mago bayan Shugaba mai ci Alpha Conde da ‘yan adawa kasar.

Kawo yanzu dai ba a sanar da sakamakon wannan zabe a hukumance ba, sai dai sakamakon da wasu tashohin radio kasar suka fara fitarwa na nuna cewa Alpha conde ne kan gaba, ko da ya ke ana tunani akwai yiwuwar komawa zage na 2.

Jagoran tawagar masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai wato EU a kasar Frank Engels ya ce duk da samun matsalolin katunan zabe, da rashin kimtsawa da kyau a wasu rumfunan zabe, an kwatata sahihanci.

Kasar Guinea dai na da tarihi rikicin siyasa a baya, kamar na shekarar 2010 wanda ya baiwa Conde Nasara, inda aka yi hargitse da ya kashe mutane 2 tare jikkata 33.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta ce an kwatatan gaskiya a zaben.

Tun a ranar litinin da ta gabata dan takara Jam’iyyar adawa kasar ke cewa a sake zaben domin babu gaskiya, Amurka dai ta gargadi masu adawa kasar kan haifar da barkewar rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.