Isa ga babban shafi
Burkina faso

Yakin neman zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisa

Da misalign karfe 12 na daren yau asabar ake kaddamar yakin neman zaben shugabancin kasa zagaye na farko da na ‘yan Majalisar dokoki a Burkina Faso, a yunkurin da ake na sake maido kasar kan turbar dimokuradiyya.

Sojoji a bikin cika shekara daya da kawar Compaore daga mulki
Sojoji a bikin cika shekara daya da kawar Compaore daga mulki AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Talla

Burkina Faso dai ta share tsawon shekara daya a karkashin gwamnatin rikon kwarya, bayan da boren al’ummar ya yi sanadiyyar faduwar gwmanatin Blaise Compaore wanda ya mulkin kasar shekaru 27.

Hakazalika yunkurin da wasu sojoji wadanda ga alama ke biyaya ga tsohon shugaban na kwace mulki a watannin da suka gabata ya ci tura, sakamakon jajircewar al’ummar kasar da kuma sauran kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.