Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun gargadi ‘Yan Biafra a Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta yi barazanar daukan matakai masu tsauri don murkushe duk wata barazanar da ke fitowa daga masu fafutukar kafa kasar Biafra a kudancin kasar.

Kwamandan Sojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Kwamandan Sojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai nigerian defence
Talla

Kwamandan runduna ta uku ta sojin kasar, Janar Hassan Umaru ne ya bayyana haka ga manema labarai a Jos, inda ya ke cewar hakkin sojoji ne su tabbatar da bin doka da oda tare da hana barkewar duk wani rikici.

Janar Umaru ya ce ba za su nade hannayensu suna kallon wasu batagari na tayar da hankali ba da kuma shirin jefa kasar cikin rikici, saboda haka idan ta kama suyi amfani da karfi za su yi don murkushe masu tada kayar baya.

Tuni dai rundunar ‘Yan sandan a Najeriya ta cafke mutane 88 wasu mambobin masu da’awar kasar Biafra a kudancin kasar wadanda suka fito suna zanga-zanga domin nuna adawa da kame shugabansu Nnamdi Kanu da ke yada manufofinsu a gidan Radion da ya bude na musamman kan Biafra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.