Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Ana ci gaba da gudanar da bincike a Burkina Faso

Hukumomi a kasar Burkina Faso na ci gaba da yi wa ministan wasanni a karkashin tsohuwar gwamnatin shugaba Blaise Compaare,Yacouba Ouedrago tambayoyi bisa zargin cewa shi ma yana da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.

Sojin Burkina Faso a fadar Gwamnatin kasar
Sojin Burkina Faso a fadar Gwamnatin kasar AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Talla

Gwamnatin Kasar Burkina Faso ta kadamar da bincike kan juyin mulkin da akayi a kasar don gano daukacin masu hannu a wannan kazamin aiki.

Firaminsitan kasar Isaac Zida ya bayyana cewar hukumar binciken shari’a a karkashin alkalin kotun daukaka karar kasar zata mayar da hankali kan wadanda suka shirya juyin mulkin, wadanda suka aiwatar da kuma sojoji da fararen hular dake da hannu a ciki.

Cikin wadanda ake sanar da kamawa akwai Janar Gilbert Diendere shugaban juyin mulkin da Djibril Bassole tsohon ministan harkokin wajen kasar a karkashin gwamnatin Blaise Compaore.

An dai kama Yacouba Ouedrago ne a ranar larabar da ta gabata, inda ya kasance mutum na biyu a cikin jami’an tsohuwar gwamnatin kasar da aka cafke bisa irin wannan zargi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.