Isa ga babban shafi
Masar

An kashe mutane 18 a gidan rawa da ke Masar

Akalla mutane 18 sun rasa rayukansu sakamakon wani bam mai haddasa gobara da aka jefa wa jama’a a wani gidan rawa da ke birnin Al-kahira na Masar kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar a yau jumma’a.

Masar na fama da hare haren yan tawaye tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Morsi
Masar na fama da hare haren yan tawaye tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Al-amarin ya faru ne a yankin Agouza da ke cikin birnin yayin da jaridun kasar suka rawaito cewa, wasu mutane uku ne rufe da fuskokinsu suka wurga bam din kafin su bai wa kafarsu iska.

Tun lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi a shekara ta 2013, ‘yan tawaye ke kaddamar da hare hare a Masar amma sun fi kai farmaki akan jami’an tsaron kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.