MDD ta la’anci harin Burundi
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi allawaddai da munanan hare haren da ‘yan bindiaga suka kai a barikin Sojoji a Burundi a safiyar Juma’a, tare da yin kiran bin hanyoyin tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke fama da rikici.
Wallafawa ranar:
Rundunar Sojin Burundi tace an yi nasarar kashe mahara 12 tare da kame wasu 21 wadanda suka kaddamar da hari da sanyin safiya a barikin Sojoji a Bujumbura.
Jekadiyar Amurka Samantha Power da ke magana da yawun mambobgin kwamitin tsaro 15 ta yi kira dukkanin bangarorin Burundi su kaucewa rikici.
Burundi dai ta fada rikici tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana kudirin zarcewa kan madafan iko karo na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu