An saki Hannibal Ghaddafi da aka sace a Lebanon
An saki Hannibal Ghaddafi tsohon dandan marigayi kanal Ghaddafi na Libya bayan wasu ‘Yan bindiga da ba a tantance ba sun sace shi a kasar Lebanon.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar tsaron Lebenon ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa an sace shi ne a yankin Bekaa lokacin da ya ke kan hanyar shiga kasar Syria.
Kuma ‘Yan sandan sun ce bayan an sake shi a Baalbek, yanzu yana birnin Beirut.
Hannibal Ghaddafi dai yana cikin iyalan marigari Kanal Ghaddafi da suka tsere zuwa Algeria bayan ‘Yan tawaye sun kwace Tripoli a lokacin yaki da gwamnatin mahaifinsa a Libya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu