Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan adawar Congo sun hade wa Kabila kai

Manyan ‘Yan siyasar kasar Janhuriyar Demokiradiyar Congo 27 cikin su har da babban dan takarar shugabancin kasar daga cikin ‘yan adawa Moise Katumbi sun hada wata kungiyar da za ta yaki tazarcen da shugaba Joseph Kabila ke shirin yi don neman wa’adi na uku.

Joseph Kabila, Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Joseph Kabila, Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo AFP PHOTO / CARL DE SOUZA
Talla

A cikin Wata sanarwa da kungiyar ‘Yan adawar ta fitar, sun bayyana aniyarsu na hada karfi da karfe don ganin shugaba Kabila bai samu nasarar bukatar da ya ke nema ba.

Kasashen duniya da dama na bayyana damuwarsu kan shirin Joseph Kabila na kaucewa yarjejeniyar da ta kawo shi karagar mulki.

A 2016 wa’adin Shugabancin Kabila zai kawo karshe a Jamhuriyyar Congo bayan ya shafe shekaru 15 yana shugabanci, amma shugaban na neman hanyoyin da zai samu damar yin tazarce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.