Isa ga babban shafi
Najeriya

An kafa kwamitin binciken rikicin ‘Yan shi’a da Sojoji

Hukumar kare hakkin bil’adama a Najeriya ta kafa kwamitin mutane biyar domin binciken rikicin da ya faru tsakanin ‘Yan Shi’a da Sojojin kasar a garin Zaria.

Sojojin Najeriya sun roki 'Yan Shi'a hanya kafin rikici ya barke
Sojojin Najeriya sun roki 'Yan Shi'a hanya kafin rikici ya barke pophherald
Talla

An ba kwamitin wa’adin watanni biyu karkashin jagorancin Tony Ojukwu domin kammala binciken faruwar al’amarin da ya janyo hasarar rayuka da dama.

Mambobin kwamitin sun hada da Haliru Adamu da Babangida Labaran da AA Yakubu da Kabiru Elayo.

An daura wa kwamitin hakkin gano abin da ya haifar da rasa rayukan jama’a da wadanda suka aikata kisan. Sannan kwamitin zai bayar da shawarwari akan inda aka keta hakkin dan adam.

Kwamitin zai yi kokarin gano wadanda suka mutu da hasarar dukiyar da aka samu a rikicin.

A ranar Assabar 12 ga watan Disemba, almajiran Malam Ibrahim Zakzaki jagoran Shi’a suka toshe hanya tare da haramtawa tawagar Babban Hafsan Sojin Najeriya wucewa zuwa fadar Sarkin Zazzau.

An dauki lokaci Sojojin na rokon ‘Yan Shi’ar su bude hanya, domin wucewa inda za su.

Sojojin sun zargi ‘Yan Shi’ar da yunkurin halaka babban Hafsan Najeriya Janar Tukur Yusuf Burutai, lamarin da ya sa suka budewa ‘Yan Shi’ar wuta.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon arangamar, ciki har da wasu shugabannin Shi’a.

Yanzu haka shugaban ‘Yan Shi’ar Malam Zakzaki yana hannun Jami’an tsaron Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.