Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Nijar

Yan takara a zaben Nijar

A Jamhuriyar Nijar yayin da Kwararri na kungiyar kasashe renon Faransa OIF suka soma aikin binciken registar masu zabe domin warware sabanin da ke akwai tsakanin ‘yan siyasar kasar dangane da sahihancinta wannan rijista, ofishin ministan cikin gidan kasar ta sanar a yau cewa an rufe karbar sunayen yan takara a zaben kasar na ranar 21 ga watan fabrairu 2016.

Talla

Akala jam'iyyoyi siyasa kusan guda goma ne suka sanar da ajiye takardun sunayen yan takarar su a ofishin ministan cikin gidan kasar.

Daga cikin su akwai Amadou Boubacar Cisse,Hama Amadou,Ibrahim Yacouba,Mahamane Ousmane,sai  Amadou Cheiffou mai mukamin sassanta yan kasar ko Mediateur wanda ya sanar da ajiye aikin na sa.
Amadou Cheffou shugaban jam’iyyar RSD Gaskiya a wata sanarwa ya nuna godiyar sa zuwa Shugaban kasar dama ya kasar, tareda cewa lokaci ya yi na sauke wanan nauyi da aka dora masa.

Ofishin ministan cikin gida zai  isar da takardun yan takarar zuwa kotun koli,wace za ta tattance  yan takara da suka dace su tsaya zaben ranar 16 ga watan fabrairu 2016.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.