Najeriya
Metuh na tsare a gidan yari
Babbar kotu a Abuja ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare kakakin Jam’iyyar PDP Olisa Metuh a gidan yarin Kuje yayin da da ake ci gaba shari’arsa kan badakalar kudaden sayo makamai.
Wallafawa ranar:
Talla
EFCC na zargin Metuh da karbar kudi Naira miliyan 400 daga ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tasaro Sambo Dasuki. Amma Metuh ya karyata zargin.
Lauyan da ke kare Metuh ya danganta matakin ci gaba da tsare shi a gidan yari a matsayin wanda ya sabawa doka.
Nan gaba ne dai Kotu zata ci gaba da sauraren kararsa a Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu