Buhari ya karrama Golden Eaglets da suka lashe kofi a China a 1985
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karrama ‘yan wasa da dama a birnin Abuja tun daga bangaren kwallon kafa zuwa kwallon Kwando da damben zamani zuwa ‘yan wasan daga nauyi da dara.
Wallafawa ranar:
Cikin wadanda aka karrama da kudi sun hada da ‘Yan wasan da suka lashewa Najeriya kofi na ‘yan kasa da shekaru 17 na farko wadanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa alkawali tun shekaru 30 da lashe kofin duniya a China.
Shugaban ya bai wa kowanne daga cikin ‘Yan wasan Naira Miliyan biyu.
‘Yan wasan dai sun lashe kofin ne a 1985 a lokacin da buhari na shugaban kasa a mulkin soja. Amma bai cika alkawalin ba saboda juyin mulkin da aka yi ma shi
Akwai wadanda suka mutu, amma daya daga cikinsu Sani Adamu ya bayyanawa RFI Hausa farin cikinsa.
“Tunawa da mu ya faranta min rai, hakan ya nuna ba a manta da mu ba”, a cewar Adamu wanda suka lashe wa Najeriya kofi a China.
Shugaba Buhari ya ce ya godewa Allah da ya sa yana raye domin samun damar cika alkawalin.
Matasa ma da suka lashe kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 a shekarar da ta gabata sun karbi kudi Naira miliyan guda da dubu dari biyu, yayin da aka ba mai horar da su Emmanuel Amuneke dubu dari tara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu