An cafke sojoji 11 bisa zargin fasa rumbun makamai
Hukumomi a Burkina Faso sun sanar da cafke jami’an tsaro 11 dukkaninsu daga runduna ta musamman da ke kare tsohon shugaban kasar Blaise Compaore, a ci gaba da binciken wadanda ke da hannu a harin da aka ka iwa wani rumbun ajiye makamai ranar juma’a da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’i a rundunar tsaron kasar Mahamadi Bonkoungou, ya tabbatar da cafke tsoffin jami’an rusasshiyar rundunar ta RSP, inda ya bukaci samun hadin-kai daga jama’ar kasar.
Yanzu haka dai akwai wasu sojoji 15 da ake ci gaba da nema, bisa zargin cewa suna da alaka da harin wanda aka kai ranar juma’a, inda suka sace bindigogi kirar kalashnikovs da kuma rokoki da ake amfani da su domin harba makamai masu linzame.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu