Isa ga babban shafi
Saliyo

Ebola: ‘Yan sanda sun yi arangama da Matasa a Saliyo

Mutane uku sun samu raunuka a wata tarzoma da ta barke tsakanin ‘Yan sanda da Matasa a kasar Saliyo bayan sun bukaci ‘Yan kasuwa su rufe shagunansu a garin Barmoi domin farautar masu dauke da cutar Ebola.

Cutar Ebola ta dawo a Saliyo bayan tabbatar da kawar da cutar baki daya
Cutar Ebola ta dawo a Saliyo bayan tabbatar da kawar da cutar baki daya AFP PHOTO / CELLOU BINANI
Talla

Rikicin ya faru ne bayan mutuwar wata a yankin mai dauke da cutar Ebola. Kuma ‘Yan sanda na neman mutane sama da 40 da suka yi mu’amula da matar mai shekaru 22.

Matasa a garin sun farwa ‘Yan sandan ne bayan sun rufe shagunansu. Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsuhuwa tare da harba bindiga akan matasan.

Matasa uku ne aka sanar sun jikkata a arangamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.