Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Jonathan ya ki yabon Buhari Kan Boko Haram

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ki yabon Shugaba Muhammadu Buhari kan nasarorin da gwamnatinsa ke samu na yaki da kungiyar Boko Haram da ta kashe mutane da dama a arewacin kasar.

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan yace da Makaman da ya sayo gwamnatin Buhari ke yaki da Boko Haram
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan yace da Makaman da ya sayo gwamnatin Buhari ke yaki da Boko Haram RFI/Awwal
Talla

Tsohon wanda ke zantawa da tashar talabijin ta France24 a ziyarar da ya kai a kasar Switzerland, ya ce ba zai yi tsokaci a game da zargin handame kudaden da aka ware domin sayo makamai da ake yi wa wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa ba bayan an tambaye shi ko zai amince an yi yakin neman zaben shi da kudaden.

Tsohon Shugaban ya ce ba zai yi tsokaci ba kan batun rashawa ko zargin wawushe kudaden sayo makamai, saboda ana bincike kuma batun na gaban kotu. Amma Jonathan ya ce nasarar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankalo ya nuna cewa gwamnatinsa ta samu nasara akan yaki da Boko Haram.

"Yin wani furuci kamar yin shishshigi ne ga ayyukan shari’a", a cewar tsohon shugaban na Najeriya wanda ya sha kaye a zaben 2015.

Jonathan ya kara da cewa a lokacin Shugabancinsa ya yi kokarin tabbatar da cewa bangaren shari’a na tafiyar da ayyukansa a cikin ‘yanci kamar yadda doka ta shata ba tare da wani katsalandan ba.

 Sai dai kuma Mista Jonathan ya ce makaman da ake amfani da su a yanzu zamanin Mulkin Buhari domin yaki da Boko Haram, gwamnatinsa ce ta sayo su.

Tsohon Shugaban ya ki yabon gwamnatin Muhammadu Buhari ga irin nasarorinta a fagen yaki da ta'addanci, bayan an tambaye shi ko zai iya yabon gwamnatin da ta gaje shi.

“Na yi imani da cewa suna amfani ne da makaman da gwamnatin da na jagoranta ta saya, saboda an ce an karkata akalar kudaden da muka ware domin sayo wasu makaman, abinda ke nufin cewa makaman da sabuwar gwamnati ke aiki da su a yau domin yaki da Boko Haram, ba wasu ba ne face wadanda muka saya’’, inji Jonathan.

Tun lokacin da aka rantsar da shi, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da rashawa, kuma yanzu tsoffin Jami'an gwamnatin Goodluck Jonathan da dama ne ake tuhuma da wawushe kudaden aka ware domin sayo makaman yaki da Boko Haram.

Baya ga batun Boko Haram, an kuma tambayi tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan kan ko ya yarda cewa jam’iyyarsa ta PDP na fama da wasu matsaloli.

‘’Eh, jam’iyyar PDP na fama da wasu ‘yan matsaloli, amma kada ku manta mun mulki Najeriya tsawon shekaru 16, lura da cewa ba ma kan karagar mulki ba mamaki a samu irin wadannan matsaloli’’

Jonathan ya kara da cewa Idan mutum na shugaba, zai kasance  kowa na sauraren shi, amma idan mutum ya bar kan karagar mulki, zai kasance abu mai wuya ga jam’iyya ta samu shugabanci kwakkwara.

Hirar France24 da Goodluck Jonathan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.