Al'ummar Uganda na kada kuri'u a zaben shugaban kasa
Al'ummar Uganda sun fara kada kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da ake gudanarwa a yau Alhamis, inda ake zaton shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni zai iya lashe zaben.
Wallafawa ranar:
An dai samu jinkiri wajen kada kuri'un da ya kamata a fara da misalin karfe 7 na safe agogon kasar yayin da jama’a suka yi dandazo a rumfunan zabe.
‘Yan takara 7 ne ke kalubalantar Museveni wanda ya shafe kimanin shekaru 30 akan karagar mulki.
A bangare guda, hukumomin kasar sun kange shafukan sada zumunta a kasar da suka hada da Facebook da Twitter saboda zaben na yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu