AU ta yaba da halayen ‘Yan Nijar
Kungiyar Tarayyar Afrika ta yaba da halayen ‘Yan Nijar kan yadda suka gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata hatsaniya ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan tsaro inda ake da ababan hawa masu yawa da ke sintiri domin ganin anyi komi cikin kwanciyar hankali.
Al’ummar Nijar kimanin miliyan bakwai da rabi ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, a kimanin mazabu dubu ashirin da biyar da ke fadin kasar.
‘Yan takara 15 ne ke fafatawa a zaben, ciki har da shugaban kasa Mahammadou Isoufou da ke neman wa’adi shugabanci na biyu.
Kuma ana zaben ne yayin da guda daga cikin ‘yan takarar kuma tsohon shugaban majalisar kasar Hama Amadou ke tsare a gidan kaso.
Shugaba Issoufou ya kada kuri’arsa tare da iyalan shi a mazaba ta farko da ke birnin Yamai, akan idon wakiliyarmu Koubra illo, kuma ta aiko da rahoto.
Rahoton Koubra kan Zaben Nijar na 2016
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu