Burundi
Ban Ki Moon zai gana da Ukurunziza
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki Moon zai ziyarci kasar Burundi gobe talata a ci gaba da yunkurin da ake na kawo karshen tashin hankalin da ake samu a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Ziyarar tana zuwa ne bayan irin ta da wakilan kwamitin sulhu suka kai inda suka bukaci shugaban kasar Pierre Nkurunziza da ya amince da shirin kai dakarun samar da zaman lafiya amma shugaban ya sa kafa ya shure.
Shugaban yace zasu dauki duk wani shiri na tura sojoji kasar a matsayin katsalandan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu