Boko Haram
Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 92 a Kumshe
Gwamnatin Kamaru ta bayyana cewa, Rundunar sojinta ta kashe mayakan Boko Haram 92 tare da ceto mutane 850 daga hannunsu a wani samamen hadin gwiwa da sojojin Najeriya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Wata sanarwa da ministan yada labaran Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya fitar ta ce, dakarun sun kai samamen ne a kauyen Kumshe na jihar Borno da ke kan iyakar kasashen biyu.
Ministan ya ce, sojojin Kamaru guda biyu sun rasa rayukansu yayin da biyar suka jikkata a samamen bayan wata nakiya ta tashi cikin kuskure.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu