Isa ga babban shafi
Mali

An zargi Keita na Mali da cin amanar kasa

Wata kungiya farar hula a Mali da ta kunshi ‘Yan jaridu ta zargi shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita da cin amanar kasa da almubazzaranci da kudaden kasa.

Ibrahim Boubacar Keita Shugaban Mali
Ibrahim Boubacar Keita Shugaban Mali Pierre Rene-Worms/RFI
Talla

Wannan ne karon farko da shugaban Mali Boubakar Keita ya fara fuskantar suka.

Wata kungiya ce da ake kira Biprem mai mambobi 344 da wasu gungun ‘Yan jaridun Mali suka kafa ke zargin shugaban da cin amanar kasa da karkatar da kudade ta hanyar da ba ta dace ba.

A ranar 1 ga watan Maris ne Kungiyar ta shigar da kokenta a gaban babbar kotun Mali kan kalubalantar Keita.

Kungiyar ta zayyana kokenta akan badakalar kudade a gwamnatin shugaban, Tare da zargin shugaban da rashin iya tafiyar da gwamnati. Kungiyar ta bukaci kotu ta yi bincike domin daukar mataki akan shugaban.

Zargin da kungiyar Biprem ta zayyana sun hada da batun sayen jirgi da shugaban ya yi da badakalar sayen takin zamani da kuma kudaden da aka karkatar da aka ware domin sayo makamai.

Zuwa yanzu dai babu martani daga bangaren shugaba Keita dangane da zargin da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.