Isa ga babban shafi
Amurka

An yankewa limamin krista daurin shekaru 40 saboda lalata da marayu

Kotu a kasar Amurka ce ta yankewa ba Amurken dake yiwa addinin krista hidima a kenya hukuncin zaman gidan yari na shekaru 40 bayan samun shi da laifin yin lalata da wasu yara 8 dake a gidan marayu na Upendo a Nairobi babban birnin kasar

Matthew Lane Durham da yaran gidan marayun Upendo
Matthew Lane Durham da yaran gidan marayun Upendo By KELLY MCLAUGHLIN FOR DAILYMAIL.COM
Talla

A lokacin da ake tuhumar Mr Durham ya amince da yiwa wasu daga cikin yaran fyade da kuma cin zarafin wasu daga cikinsu sai dai kuma daga baya ne Mr Durham ya sakala laifin da aikin ibilis cewar bai ma tuna da lokacin da ya aikata wadannan laifufukan da ake zarginsa dasu ba.

A watan Yunin bara kotun tarraya a Amurka ta sami Mr Durham mai shekaru 21 da laifufuka har 17 da suka kunshi bata sunan kasa da kuma anfani da matsayinsa wajen yin lalata da fyade akan yara marayu, kotu ta kuma ci Mr Durham tarar kudi $15,863

Matthew Lane Durham dai ya aikata laifufukan lalata da yaran 8 cikinsu da maza da mata dake da shekaru tsakanin  4 zuwa 8  a shekara 2014 a lokacin da yake aikin yiwa addinin krista hidima a gidan marayun dake Kenya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.