Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An samu wata Mata da laifin satar jaririya shekaru 20 da suka gabata

Wata Kotu a kasar Afrika ta kudu ta samu wata mata da laifin satar jaririya tare da shayar da ita na tsawon shekaru 17 kafin daga baya Allah ya sa yarinya ta hadu da asalin iyayenta.

Bayan shafe shekaru 17 Allah ya sa Wata yarinya da aka sace ta hadu da asalin iyayenta.
Bayan shafe shekaru 17 Allah ya sa Wata yarinya da aka sace ta hadu da asalin iyayenta. Photograph: AP via guardian
Talla

Alkali mai shari’a a kotun Cape Town John Hlophe ya karyata kalaman matar yar shekaru 50 da ta sace jaririyar shekaru kusan 20, bayan ta yi ikirarin cewa an mika ma ta jaririyar ne a wata tashar jirgin kasa karkashin wani tsari na mallakar ‘ya’ya.

Alkalin ya danganta kalaman matar a matsayin tatsuniya.

Sannan kotun ta kama ta laifin zamba karkashin dokokin yara a Afrika ta kudu bayan ta yi rijistar jaririyar a matsayin ‘yarta.

A bara ne dai yarinyar ta hadu da asalin iyayenta, bayan ta kulla abota da wata yarinya a makaranta, da su ke kama da juna.

Gwaji da aka gudanar kuma ya tabbatar da cewa ‘yan matan biyu ‘yan uwan juna ne, kuma yayar ce aka sace da iyayenta suka rada wa suna Zephany Joy.

Kotun Cape Town dai ta ki bayar da belin matar da ta sace jaririyar sannan an tsayar da ranar 30 ga watan Mayu domin yanke mata hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.