Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobara ta yi barna a kasuwar Sabon Gari da ke Kano

A birnin Kano da ke Arewacin Najeriya wata mummunar gobara da ta tashi a tsakaddaren jiya a shahararriyar kasuwar nan ta Muhammadu Abubakar Rimi wadda aka fi sani da suna Sabon Gari ta kone shaguna fiye dari shida.

Kofar kasuwar Sabon-Garin, a Kano, Najeriya
Kofar kasuwar Sabon-Garin, a Kano, Najeriya
Talla

Gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 12 da rabi na daren jiya, ta shafe sa’o’I sama da 12 tana ci, inda jami’an kashe gobara ke ta kai kawon murkushe ta tare da samun taimakon wasu kamfanoni masu zaman kansu.

Har zuwa karfe 2 na ranar yau da wakilin mu na Kano ya bar kasuwar, wutar na ci gaba da ci, kuma jami’an kashe gobara na ci gaba da kokarin kashe ta.

Kawo yanzu dai ba a kai ga iya kiyasta asarar da aka tafka a gobarar ba, amma ana hasashen cewar dukiyar biliyoyin naira ce ta salwanta.

A wani taron manema labarai, Gwamnan jihar ta Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya danganta yawan tashin gobara a kasuwannin da rashin wadatattun hanyoyin a cikin kasuwannin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.