Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

MDD na zargin Sojojin Burundi da Morocco a Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya tace ta samu wani sabon zargin cin zarafin mata da ake yi wa sojojin kasahsen Burundi da Morocco da ke aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya
Dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Kakakin Majalisar Stephane Dujarric yace ana zargin wani sojan Burundi da yi wa wata yarinya mai shekaru 14 fyade a farkon wannan wata, yayin da ake zargin wani sojan Morocco da mu’amala da wata mata.

Jami’in yace tuni aka shaidawa kasashen su, bayan an kaddamar da bincike.

Tun tuni ake zargin Sojojin wanzar da zaman lafiya ciki har da dakarun Faransa da yin lalata da yara mata a jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.