CHADI
Gwamnati ta haramtawa yan adawa gudanar da zanga zaga a Chadi
Yan Sanda a kasar Chadi sun sake kama wani shugaban matasa kwana guda kafin gudanar da zanga zangar adawa da gwamnati dangane da shirin zaben kasar da za’ayi a karshen wannan mako.
Wallafawa ranar:
Talla
An kama Albissaty Salhe Alazam, daya daga cikin shugabanin kungiyar dake adawa da cigaba da zaman shugaba Idriss Deby a karagar mulki .
Bertrand Sohhoh Ngandjei, daga kungiyoyin fararen hula yace kamun ya tabbatar da aniyar gwamnati na murkushe demokradiyar kasar.
Za a dai gudanar da zaben kasar Chadi ranar 10 ga watan Afrilun nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu