Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta nemi hadin kan kasashen Sahel kan yakar ta’addanci

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce akwai bukatar yin aiki tare tsakanin kasar da kuma rundunar hadin-gwiwa ta kasashen yankin Sahel, domin fada da ayyukan ta’addanci musamman a wannan yankin Afirka.

Shugaban Burkina Faso Marc Christian Kabore ya kai ziyara Faransa
Shugaban Burkina Faso Marc Christian Kabore ya kai ziyara Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Hollande ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Burkina Faso Christian Kabore wanda ya kai ziyara a birnin Paris.

A cewar shugaba Hollance ya kamata a yi la’akari da ta’addanci abu ne da ke iya shafar kowace kasa, musamman wadanda aka tabbatar da cewa an samu kafuwar kungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi, irinsu Mali, wanda ya zama wajibi a kulla kawance da kasashen domin yaki da ayyukan ta’addanci.

Hollande yace Faransa za ta yi aiki da kasashen da ake kira gungun G5 da ke yankin Sahel, wajen musayar bayanan sirri.

Sannan ya kara da cewa babu wata kasar da ke iya cewa ta wadaci kanta ta fannin tsaro a irin wanan yanayi, yin aiki a tare na nufin cewa kasashe sun yarda da juna dangane da kokarin da suke yi wajen tabbatar da tsaro da kuma kare kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.