Isa ga babban shafi
Madagascar

Firimiyan Madagascar ya yi murabus

Firaministan Madagascar Jean Ravelonarivo ya bayyana yin murabus tare da rusa gwamnati sakamakon takaddamar da ke tsakanin shi da shugaban kasa Hery Rajaonarimampianina.

Jean Ravelonarivo Firaministan Madagascar
Jean Ravelonarivo Firaministan Madagascar AFP PHOTO / RIJASOLO
Talla

Wannan dai wani mataki ne da ake ganin zai rura rikicin siyasa a kasar bayan sasanta shugabannin biyu a zaben da ya gabata.

Tuni fadar shugaban kasa ta sanar da amincewa da murabus din Firaminista Jean Ravelonarivo.

Hery Rajaonarimampianina wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2013 na fuskantar suka daga ‘Yan adawa kan tafiyar da gwamnati, musamman wajen gudanar da ayyukan ci gaba da matsalar tabarbarewar tsaro.

Madagascar dai ta yi fama da rikicin siyasa tun lokacin da aka hambayar da gwamnarin Ravalomanana a 2009.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.