Riek Machar zai koma birnin Juba
Madugun ‘yan tawaye kuma tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar ya ce zai koma birnin Juba a ranar 18 ga wannan wata, karo na farko bayan fice warsa daga birnin a watan disambar shekara ta 2013.
Wallafawa ranar:
Bayan ya isa a Juba ne za a yi bikin kafa sabuwar majalisar ministoci ta gwamnatin rikon kwarya tsakanin Riek Machar da kuma Salva Kiir.
Sama da mutane 150,000 ne suka tserewa gidajensu a rikicin Sudan ta kudu da ya tursasawa sama da mutane miliyan biyu gudun hijira.
A na sa rai dai dawowar Machar tare da kafa gwamnatin hadaka zai kawo karshan zub da jini da tashin hankalin da kasar ta tsinci kanta a ciki shekara biyu bayan balewar daga Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu