Kasashen Duniya 50 Na Taro Don Taimakawa Libya
Wakilan kasashen duniya 50 na wani taro a birnin Tunis na kasar Tunisiya domin muhawara gameda irin gudunmawar da za su bayar domin karfafa wa Gwamnatin hadin kai na kasar Libya.
Wallafawa ranar:
Taron na kwana daya ya kasance Majalisar Dunkin Duniya da kuma kasar Britaniya suka shirya da niyyar ganin an baiwa Gwamnatin hadin kan kasar Libya damar warware tsarin ta na sake gina kasar bayar yaki na tsawon shekaru biyar.
Fayez al-Sarraj, shugaban Gwamnatin Hadakan ya isa birnin Tripoli ta jirgin ruwa, makonni biyu da suka gabata, tare da rakiyar Dakaru na musamman da suka kunshi sojan ruwa, kuma har ya sami amincewar wasu Hukumomin kasar.
Wakilan kasashe 40 suka halarci zaman taron na Talata a Tunis sai kuma kungiyoyi daban-daban na duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu