Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Karancin ruwan sha a Burkina Faso

Mutanen birnin Ouagadougou a kasar Burkina faso na fuskantar karancin ruwan sha,rahotani daga birni na nuni cewa mutanen wasu unguwani sun damu gani ta yada lamarin ya kazanta. 

Ruwan sha
Ruwan sha RFI
Talla

Gwamnati ta bakin ministan mai kula da ruwan sha Niouga Ambroise Ouedrago,hukumomin za su shawo kan wannan matsala,a gagauce Gwamnati ta umurci ma’aikantan dake da nauyi warware wannan matsala samar da ruwa lokaci zuwa lokaci a wasu unguwanin birnin Ouagadougou.
  Idan aka yi tuni Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi cewa, matukar ba’a samu sauye sauye ba, al-ummar duniya na iya fadawa cikin matsalar rashin ruwan sha, lamarin kuma, zai fi yin illa ga kasashe masu fama da zafi.

A wani rahotan da take fitarwa duk shekara, majalisar tace, ta damu da yadda ake bannatar da ruwa, kuma in aka ci gaba a haka, za' a yi hasarar ruwan shan da ake dashi, da kashi 40 cikin 100, nan da shekara ta 2030.

Majalisar tace, hakikanin gaskiya akwai ruwan da zai isar da bukatun kowa a duniya, abinda kawai ake bukata, shine a sauya yadda ake amfani da kuma rarraba shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.