Isa ga babban shafi
Najeriya

Fetir zai koma Naira 145 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cire tallafin mai kuma daga yanzu farashin fetir zai koma Naira 145 kamar yadda karamin Ministan albarkatun Mai ya sanar a yau Laraba.

Emmanuel Ibe Kachikwu Ministan Mai a Najeriya
Emmanuel Ibe Kachikwu Ministan Mai a Najeriya AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Matakin na zuwa ne bayan wata ganawa tsakanin Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Ministan Mai Dr Ibe Kachikwu da shugabannin Majalisar Tarayya da kungiyoyin kwadago da kuma kungiyoyin dakon Mai a Najeriya.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar tace ya zama wajibi ta dauki matakin domin samun wadatuwar mai ga ‘yan kasa.

Sannan matakin zai taimaka a farfado da matatun mai tare da bude kofa ga kamfanonin kasashen waje su zuba jari.

Nan gaba dai za a kayyade farashin da za a sayar wa 'Yan Najeirya wanda Ministan yace ba zai wuce Naira 145 ba.

Yanzu kowa na da ‘yancin shigo da man a Najeriya karkashin sabbin matakan da gwamnati tace a nan gaba zai sa farashin man ya sauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.