Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta sassauta tarar da ta ci MTN

Yanzu Kamfanin sadarwa na MTN zai biya tarar Dala biliyan daya da miliyan 700 maimakon Dala biliyan uku da miliyan dari 900 da gwamnatin Najeriya ta ci kamfanin tara a baya.

Ofishin kamfanin sadarwa na MTN
Ofishin kamfanin sadarwa na MTN 8brand.co
Talla

Gwamnatin Najeriya ta soma daukar matakin ne bayan samun kamfanin na MTN da laifin kin datse layukan mutane miliyan biyar da bai yi wa rijista ba, da ita gwamnati ta ce ya amfanar da mayakan Boko Haram wajen gudanar da ayukansu.

Tuni dai ‘yan majalisar wakilan kasar suka yi watsi da ragin, a yayin da suma masu amfani da layin na MTN ke adawa da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.