Isa ga babban shafi
Benin

Boko Haram: Benin ta yi shirin ko-ta-kwana

Jamhuriyar Benin ta sanya jami’an tsaron ta cikin shirin ko-ta-kwana domin magance duk wata barazanar tsaro da kan iya tasowa a kasar. Sakamakon barazanar yunkurin kai wa kasar harin ta’addanci.

Sojojin Benin na cikin rundunar da ke fada da mayakan Boko Haram na Najeriya
Sojojin Benin na cikin rundunar da ke fada da mayakan Boko Haram na Najeriya wikimedia
Talla

Shugaban rundunar sojin kasar Janar Awal Nagnimi ya shaidawa Radio France Internationale cewar matakin ya biyo bayan wasu bayanan asirin da suka samu.

Jamhuriyar Benin na daga cikin kasashen da suka bada gudumawar sojoji don yaki da kungiyar Boko Haram mai da’awar Jihadi a Afrika.

Tun a makon jiya gwamnatin Benin ta fara tsaurara tsaro a kan iyakokinta bayan wasu kasashen waje sun gargadin ana iya kai wa kasar da ke makwabtaka da Najeriya da Nijar hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.