Isa ga babban shafi
Mali

Za a kara yawan dakaru 2,500 a Mali

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ya kara yawan dakarun samar da zaman lafiya da ke aiki a Mali da sojoji 2500 domin magance kazamin harin da ake kai wa kan sojojin.

Rundunar Minusma à Tombouctou, na Mali.
Rundunar Minusma à Tombouctou, na Mali. Sebastien RIEUSSEC / AFP
Talla

Jakadan Faransa a kwamitin Francois Delattre ya ce Karin zai taimakawa sojojin da ke aikin wajen murkushe duk wata barazana da kan iya tasowa daga mayakan da ke da’awar Jihadi a Mali

Cikin kasashen da za su bada gudumawar sojoji har da Jamus da zata tura sojoji 650.

Faransa ce ta gabatar da kudirin wanda yanzu dakarun MINUSMA za su kai dakaru 15,200 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali.

Yanzkin arewacin Mali dai na cikin barazanar mayakan Al Qaeda da wasu kungiyoyin Jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.