Isa ga babban shafi
Nijar

Ana bikin Sallah a Nijar

A yau Talata Al’ummar Nijar ke gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr bayan ganin jinjirin watan Shawwal Yammacin jiya. Amma a Najeriya da Saudiya da wasu kasashen Larabawa na kammala azumin Ramadana ne a yau.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da tsohon Firaministansa Birji Rafini da Tsohon shugaban Majalisa Hama Amadou a sahun gaba a wata Sallar Idi
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da tsohon Firaministansa Birji Rafini da Tsohon shugaban Majalisa Hama Amadou a sahun gaba a wata Sallar Idi Laura-Angela Bagnetto
Talla

Firaminista Birji Rafini ne ya sanar da ganin watan na Shawwal a Jamhuriyar Nijar tare da Majalisar Malamai ta kasa bayan ganin watan a Diffa da Zinder.

A jawabinsa na Barka da Sallah, Firaministan ya ce Allah ya karbi addu’arsu ta neman damina mai albarka da kuma nasarar yaki da Boko Haram a cikin azumin watan Ramadan, tare da bayyana fatar al’ummar Nijar za su yi sallah lafiya.

Sai dai a Najeriya da Saudiya da wasu manyan kasashen Larabawa sun cika azumi ne 30 a yau Talata sakamakon rashin ganin watan Shawwal inda sai gobe za a yi sallah eid el fitr a kasashen.

Wakilin RFI daga Maradi Salissou Issa ya aiko da rahoto kan ganin watan Shawwal a Nijar.

01:13

An ga watan Shawwal a Nijar

Salisu Isah

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.