Isa ga babban shafi
Najeriya

PENGASSAN na yajin aiki a wannan alhamis

Kungiyar PENGASSAN wadda ta kunshi manyan ma’aikatan mai a Najeriya ta kira magoya bayanta da su fara yajin aiki daga wannan alhamis domin neman a warware wasu matsaloli da suka shafi harkar mai a kasar.

Gidan mai mallakin NNPC a Najeriya
Gidan mai mallakin NNPC a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Mai Magana da yawun kungiyar Emmanuel Ojugbana, ya ce taron da manyan jami’an kungiyar suka gudanar a larabar da ta gabata, ya bukaci illahirin magoya bayanta su fara yajin aikin, lura da yadda gwmanati ta gaza biya ma su bukatunsu duk da cewa an gudanar da tattaunawa har sau biyu tsakanin bangarorin biyu a cikin watan jiya.

Yanzu haka dai an fara fargaba a game da irin illolin da wannan yajin aikin zai iya haifarwa kasar a daidai lokacin da aka shiga wata na biyu da fara amfani da sabon da farashin mai ba tare da an yi karancin sa ba a kasuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.