Afrika ta tsakiya na cikin hatsari- Touadera
Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera ya ce har yanzu kasar shi na cikin hatsari saboda yadda wasu yankunan kasar ke hannun kungiyoyi masu dauke da makamai.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya fadi haka ne a yau Lahadi a yayin da ya ke cika kwanaki 100 da zaben shi a matsayin shugaban kasa.
A watan Fabrairu ne aka zabi Touadera da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan shafe shekaru ana rikici.
Shugaban ya ce zasu yi kokarin bin matakan da suka dace domin ‘yanto kasar tare da taimakon dakarun kasashen Faransa da na Afrika da wasu kasashen duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu