Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar na son a kafa rundunar yaki da ta’addanci

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issofou ya gabatar da bukatar kafa wata rundunar soji don yaki da ta’addanci a kasashen Afirka ta Yamma da ke fuskantar barazana daga Boko Haram da mayakan Jihadi a Mali.

Shugabannin kasashen kungiyar Conseil de l'entente a taron da suka gudanar a Yamai
Shugabannin kasashen kungiyar Conseil de l'entente a taron da suka gudanar a Yamai aouaga.com
Talla

Yayin da ya ke jawabi wajen taron kungiyar Conseil de l’entente ta shugabanin kasashen Cote d’Ivoire da Benin da Burkina Faso da Togo a birnin Yammai, shugaba Issoufou ya bukaci karfafa rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta MUNISMA da ke aiki a Mali don kai dauki duk lokacin da aka samu harin ta’addanci a Yankin.

Taron ya samu halartar shugaba Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire da Roch Marc Christian Kabore na Burkina Faso da Patrice Talon na Benin da Faure Gnassingne na Togo.

Shugaban ya ce ya zama dole kasashen da ke Yankin yammacin Afrika su hada kansu domin fuskantar matsalar Ta’addanci da ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar su.

Akwai dai rundunar hadin-kai ta kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Benin da kuma Kamaru da aka kafa domin fada da mayakan Boko Haram a tafkin chadi.

Rundunar ta kunshi dakaru 8,500 daga kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi da kuma Benin.

Shugaba Issoufou ya ce irin hare haren da aka kai a otel otel a manyan biranen Mali da Cote d’Ivoire da Burkina Faso ya tabbatar da bukatar kafa rundana ta musamman.

Boko Haram dai na ci gaba da zama babbar barazanar tsaro ga kasashen yammacin Afrika bayan ta fadada yakinta daga Najeriya zuwa Nijar da Kamaru da Chadi.

 

01:31

Taron Kungiyar Conseil de l'entente a Yamai

Lydia Ado

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.